<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>109</hymn_number>
<title>Jama'a Duk, Ku Zo Mu Yi Yabo Ga Allahnmu LW109</title>
<lyrics>[V1]
 1) Jama'a duk, ku zo mu yi yabo ga Allahnmu.
 Mu gode domin Yesunmu ya ɗauke laifinmu.

[V2]
 2) Shari'armu mutuwa ce, Yesu ya ɗauke duk.
 Ya ba da ransa dominmu, domin ya fanshe mu.

[V3]
 3) An kafa shi da ƙusoshi a bisa giciye,
 Ba domin laifofinsa ba, amma don namu ne.

[V4]
 4) Yanzu ko ranar mutuwa, ba zan ji tsoro ba.
 Yesu ya ɗauke laifina, ba zai kāshe ni ba.</lyrics>
</song>